Shugaba Obama zai wuce taron kungiyar G8

Shugaba Obama yana jawabi ga Majalisun Burtaniya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama yana jawabi ga Majalisun Burtaniya

A yau ne Shugaba Obama na Amurka, wanda ke kawo karshen ziyarar da ya kai Burtaniya, zai tashi zuwa Faransa shi da mai dakinsa, inda zai halarci taron kolin kasashen duniya takwas masu karfin tattalin arziki, wato G8.

Taron dai na shugabannin kasashen Amurka, da Canada, da Japan, da Rasha, da kuma manyan kasashen Turai hudu ne.

Tuni aka fara aza ayar tambaya a kan tasirin taron a wannan zamani da wadansu kasashe masu tasowa ke fadada tasirinsu ta fuskar tattalin arziki.

Sai dai al'amuran da ke faruwa a Arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya, da ma bala’in nukiliya a kasar Japan, sun karawa kasashen takwas kaimi.

Da farko dai alamu sun nuna cewa taron kolin na bana, wanda za a gudanar a Deauville, wani wurin shakatawa na bakin tekun Faransa, ba zai yi armashi ba.

Amma, kamar yadda Shugaba Obama ya nuna a Landan jiya, kungiyar manyan kasashen ta samu karin karsashi.

Tuni dai al'amura suka mayar da burin kungiyar na warware matsalar talauci da kuma sauyin yanayi a duniya tsohon zance; a maimakon haka, taron na yau zai mai da hanakli ne a kan batutuwan da suka hada da sababbin kalubale na siyasa.

Za su kuma tattauna a kan ko ya dace a sake tunani a kan kiyaye hadarin nukiliya idan aka dubi bala’in da ya auku a Japan; kuma ko ya dace a kara sanya ido a kan hanyar sadarwa ta intanet ko kuma a kyale kowa ya sakata ya wala.

Wani batun mai muhimmanci kuma da za su tattauna shi ne yadda za a warware matsalar siyasar Libya da kuma yadda ya kamata a tunkari sauye-sauyen da aka samu a Masar da Tunisia—da samawa kasashen biyu tallafin biliyoyin daloli don taimaka musu tsayawa da kafafuwansu a bisa tsarin dimokuradiyya.

Karin bayani