An kashe wani jami'in gwamnatin Iraki

Firayim Minista Nouri Al-Maliki Hakkin mallakar hoto p
Image caption Firayim Minista Nouri Al-Maliki na Iraki

Wadansu ’yan bindiga sun hallaka mutumin da ke aikin zakulowa, da kuma kawar da masu alaka da tsohuwar gwamnatin marigayi Saddam Hussein a Iraki.

Jami'an tsaro sun ce an harbe Ali al-Lami ne har lahira yayin da ya ke tuka mota a gabashin birnin Bagadaza.

Ko a bara dai Ali al-Lami, wanda ke da alaka ta kut da kut da gwamnatin 'yan Shi'a ta Iran, ya haramtawa ’yan siyasa ’yan Sunni da dama tsayawa takarar zaben majalisar dokoki a bisa zargin suna da alaka da tsohuwar jam'iyyar Ba'ath.

Masu aiko da rahotanni sun ce a matsayinsa na shugaban Hukumar Tabbatar da Gaskiya Adalci, Mista al-Lami na da makiya masu dimbin yawa.