Likitoci za su duba lafiyar Ratko Mladic

'Yan sanda na yiwa Ratko Mladic rakiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda na yiwa Ratko Mladic rakiya

A yau wadansu likitoci za su yanke shawara a kan ko tsohon kwamandan sojojin Sabiyawan Bosniya, Ratko Mladic, yana da koshin lafiyar da zai ci gaba da gurfana a gaban wata kotu ta musamman.

Kotun dai na sauraren bahasi ne a kan ko za a mika Mista Mladic ga Kotun Hukunta Laifukan Yaki ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Hague.

An dakatar da zaman kotun ta musamman ne jiya Alhamis bayan lauyan Mista Mladic ya ce tsohon kwamandan Sabiyawan Bosnian ba shi da isasshiyar lafiya.

Lauyan, Milos Saljic, ya ce alkalin kotun ya so ya kammala yiwa Mista Mladic tambayoyi, amma hakan bai samu ba, saboda laulayin da Mista Mladic ya ke fama da shi.

Yanzu haka dai shekarun Mista Mladic sittin da tara, kuma ya nuna alamun rauni lokacin da ya shiga kotun yana daga kafa da kyar.

Ko an ci gaba da sauraron bahasin dai za a dauki kusan mako guda kafin a kai Mista Mladic kotun ta Majalisar Dinkin Duniya; mai yiwuwa kuma sai bayan watanni goma sha takwas za a fara yi masa shari'a.

Ana dai tuhumar Mista Mladic ne dangane da kisan kare dangin da ake zargin dakarun Sabiya da ke karkashin jagorancinsa sun aikata a Bosniya a shekarar 1995.