'Yan adawa sun kaurcewa gyaran doka a Nijar

Taswirar Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Taswirar Jamhuriyar Nijar

'Yan Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijar sun yiwa dokar da ta kayyade matsayin adawa a kasar gyaran fuska, a ayoyin doka na sha hudu da sha biyar masu magana a kan yadda ya kamata kwamitocin gudanarwa na kananan hukumomi su kasance.

Sai dai 'yan majalisar masu rinjaye kadai ne suka kada kuri'ar amincewa da sauye-sauyen, yayin da na bangaren adawa suka kaurace.

Alhaji Tijani Abdulkadir, shugaban rukunin 'yan majalisar MNSD Nasara mai adawa, ya shaidawa BBC dalilinsu na kauracewa:

“Kamar kuduri na sha hudu—yadda aka yi shi da farko, ya shafi majalisa da kuma kananan hukumomi.

“Kwaskwarimar da suka yi sai cire wannan abu suka maido shi kan majalisa kadai.

“...[Wannan shi ya sa] ba mu sa wa [dokar] hannu ba, mun ce ba mu yarda da ita ba”.

’Yan adawa na kuma ganin an yi gaggawa wajen yiwa dokar kwaskwarima tunda ba a ma fara amfani da ita ba balle a san inda ta ke da matsaloli.

Sai dai a cewar Alhaji Shafi’u Magarya, wani majalisa na jam’iyyar PNDS Tarayya mai mulki, akwai bukatar kawo wannan gyara tun da wuri.

“Shi da kan shi shugaban ‘yan adawa, Alhaji Seini Oumar, an gayyace shi ya shiga gwamnati suka ce a’a za su zauna su yi aikinsu na dawa.

“Ke nan bai kamata a ce a wadansu wurare kamar majalisa babu adawa ba—ya zama mulkin game-baki ke nan, wanda zai bayar da damar a cuci talakawa.

“Wannan ne muka guda, shi ya sa muka kawo wannan gyaran fuska”, in ji Alhaji Shafi’u.