Kalubalen da ke gaban gwamnatin Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Yayin da ake shirye-shiryen rantsar da shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ranar Lahadin da ke tafe, wani kalubale da zai fuskanta shi ne na samar da wutar lantarki, wacce ke da matukar muhimmanci ga rayuwar al'umma, da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.

A baya dai gwamnatocin kasar ta Najeriya sun sha yin ikirarin daukar matakan shawo kan matsalar wutar lartarkin wadda ta addabi 'yan kasar, amma har yanzu ba a ga wani sauyi ba.

Najeriya dai ita ce kasar da ta fi kowacce kasa yawan jama'a a nahiyar Afirka, amma kuma ta kasa shawo kan matsalar wutar lantarkin, kuma hakan ya sa ko da wadansu kananan kasashen Afirka sun shiga gabanta ta fuskar walwalar jama'a da kuma ci gaban tattalin arziki.

Malam Umar Yunus, wani dan jarida mai zaman kansa, kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, yana ganin cewa kasashen da ke tashe a duniya yanzu sun bunkasa ne saboda sun bayar da fifiko ga harkar samar da makamashi:

“Kasashen da suka ci gaba da kuma wadanda ke tasowa—misali China, da India, da kuma Brazil—za ka ga cewa da makamashi su ke tinkaho...[domin] idan babu wannan makamashin za a dukushe, kamar yadda yanzu a Najeriya rashin makamashin ya durkusar da masana’antu da sana’o’i daban-daban, manya da kanana”.