Obama zai yi jawabi kan Gabas ta Tsakiya

Shugaba Barack Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

Shugaban Amurka, Barack Obama, zai yi wani jawabi nan gaba a yau, inda zai bayyana shirinsa a kan yankin Gabas ta Tsakiya.

Ana tsammanin Mista Obama zai bayyana cewa wannan wata dama ce da aka samu a bakidayan yankin, kuma Amurka za ta ci gaba da goyawa dimokuradiyya baya, da kuma zanga-zangar lumana da kare hakkin dan-Adam.

Ana kuma tsammanin zai bayar da sanarwar wani tallafi ga kasashen Tunisia da Masar, domin kawai ya nuna cewa Amurka za ta bayar da lada ga duk kasar da ta rungumi sauyi.

Ana tsammanin shugaban na Amurka zai kuma bayyana cewa bayan kisan Osama bin Laden da kuma karshen yakin Iraki, yankin zai samu kyakkyawar makoma.