'Jawabin Obama yaudarar kai ne' -Gaddafi

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Mutane da dama ne a yankin Gabas ta Tsakiya suka saurari jawabin Shugaba Barack Obama na Amurka wanda a ciki ya zayyana manufofin Amurka a kan yankin da ma sauran kasashen Musulmi.

Shugaban na Amurka ya goyi bayan kafa kasar Falasdinu a bisa iyakokin shekarar 1967.

Mista Obama ya kuma bayyana goyon baya ga al'ummomin kasashen yankin wadanda suke bore, musamman ma a Libya da Syria.

A jawabin nasa, Shugaba Obama ya ce lokaci ya kusa kurewa Kanar Gaddafi, ko da ya ke bai nanata kira ga shugaban na Libya ya sauka daga mulki nan take ba.

Sai dai a cewar wani mai magana da yawun Shugaba Gaddafi Mista Obama yaudarar kansa kawai ya ke yi don kuwa ba shi da ikon yanke hukuncin cewa Kanar Gaddafi ya sauka ko ya ci gaba da mulki.

Kakakin na gwamnatin Libya ya kuma yi kira ga Amurka da sauran kasashen Kungiyar Tsaro ta NATO su rungumi shirin samar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka, wanda ya tanadi cewa sojojin Libya su janye daga biranen da suke rike da su idan 'yan tawaye suka ajiye makamansu.

A daidai lokacin sai karar fashewar wani abu ta girgiza dakin da kakakin ya ke magana.

Jami'an kasar ta Libya sun kewaya da manema labarai wurin da al'amarin ya faru a tashar jiragen ruwa ta Tripoli inda harshen wuta da hayaki ke tashi daga wani abin da ya yi kama da karamin jirgin ruwan yaki.