An hallaka akalla mutum guda a Pakistan

Daya daga cikin motocin da bom din ya tashi da su Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Daya daga cikin motocin da bom din ya tashi da su

Akalla mutum guda aka hallaka, bayan fashewar wani abu a birnin Peshawar da ke kasar Pakistan, mutane da dama kuma suka samu raunuka.

'Yan sanda sun ce wani bom ne ya fashe a gefen titi, kuma ya tashi da wadansu motocin kasar Amurka guda biyu.

Wani mai magana da yawun ofishin jakadancin kasar ta Amurka ya ce daya daga cikin motocin ta yi dameji.

Wadanda suka shaida faruwar al’amarin sun ce abin ya tona wani katon rami a gefen titin.

Birnin Peshawar dai—wanda ke arewa maso yammacin Pakistan—yanki ne da 'yan bindiga suke yawan kaiwa hari.