Dubban matasa na zanga-zanga a SPain

Dubban masu zanga-zanga a Spain Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban masu zanga-zanga a Spain

Dubban masu zanga-zanga a Spain sun yi biris da haramcin hukumar zabe ta kasar sun yi cincirindo a wani dandali da ke tsakiyar birnin Madrid cikin dare.

Kwanaki shida da suka wuce ne dai aka fara zanga-zangar, ta kuma yadu zuwa biranen kasar a karkashin jagorancin matasan da ke nuna takaicinsu da rashin aikin yi, da cin hanci da rashawa da kuma yadda a tunaninsu 'yan siyasa ba sa wakiltar su.

Sai dai wannan ne taro mafi girma kawo yanzu, kuma wannan karon, taron na masu zanga-zanga a dandalin Puerta del Sol haramtacce ne.

'Yan sanda sun ce masu zanga-zanga dubu ashirin da biyar ne suka yi kunnen uwar shegu da haramcin suka yi dafifi a dandalin suka kuma cika titunan da ke kewaye da dandalin.

A daidai lokacin da haramcin ya fara aiki da tsakar dare an yi tsit na dan wani lokaci, sannan sai mutanen da suka taru suka barke da shewa da wake-wake.

Wannan zanga-zanga dai ta fara ne daga zaman dirshen a tsakiyar birnin Madrid na wasu matasan kasar wadanda takaici ya ishe su na rashin aikin yi da kuma jin cewa manufoin gwamnati na ba da kariya ga kasuwannin hada-hadar kudade fiye da al'ummar kasar.

Daruruwan mutane ne dai ke yin sansani a dandalin ko wanne dare tun ranar Lahadin da ta gabata, da rana kuma su shiga tafka doguwar muhawara.

Hukumar zabe ta kasar dai ta yanke hukuncin cewa a tarwatsa masu zanga-zangar da tsakar daren jiya don a samu abin da ta kira “kwana guda na zuzzurfan tunani” kafin zabubbukan kananan hukumomin da za a gudanar gobe Lahadi.

Sai dai ya zuwa yanzu 'yan sanda ba su tsoma baki a wannan al'amari ba, kuma zaman dirshan din sai karuwa ya ke yi ba karewa ba.