An kashe sama da mutane 20 a Yemen

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Sama da mutane 20 ne suka mutu a fafatawar da akayi tsakanin jami'an gwamnati da 'yan adawan a babban birnin Yemen wato Sana'a.

Kusan mutane tamanin ne dai aka kashe tun ranar litinin da aka fara fada tsakanin gwamnati da 'yan adawa, kuma guda bayan Shugaban kasar Ali Abdullah Saleh yaki sa hannu a wata yarjejiniya da zai sa ya sauka daga kan mulki.

Yayin da ake ci gaba da kazamin fada tsakanin jami'an tsaro da kuma dakarun kabila mafi girma a kasar Yemen, Amurka ta umurci jami'an diflomasiyyar ta wadanda zamansu bai wajaba ba da ma sauran Amurkawa su bar kasar ta Yemen.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Amurka, barazana ta karu matuka ta fuksar tsaro saboda tashe-tashen hankula da kuma ayyukan ta'addanci a kasar.

Fadan dai ya tilasta rufe filin saukar jiragen sama na birnin Sanaa, bayan an kwashe kwanaki uku ana ba-ta-kashi, al'amarin da ya jawo akalla mutane sittin suka rasa rayukansu.

Wani dan jarida a kasar, Tom Finn, ya shaidawa BBC cewa yanayi a birnin Sanaa ya kara kazancewa.

“Ina kan rufin wani dogon gida. Gaba daya birnin yana cikin duhu; sai dai ina ganin walkiya, ina kuma jin karar rokoki da manyan bindigogi.

“Ina kuma ganin walkiyar wadansu jajayen abubuwa a sama wadanda suka yi kama da makaman kakkabo jiragen sama”.

Shugaban kasar ta Yemen, Ali Abdullah Saleh, ya yi kememe ya ki sauka daga kan mulki, yana mai cewa ba zai bari kasarsa ta fada cikin halin ni-'yasu ba.

Sai dai wani tsohon mashawarcin gwamnati, wanda ya koma bangaren 'yan adawa, Dakta Muhammad Qubati, ya ce manufar Shugaba Saleh ita ce yiwa kasar sakiyar da ba ruwa.

“Yunkuri ya ke yi ya fasa, kowa ya rasa, in ya so sai ya sulale ya yi tafiyarsa.

“Ba shakka manufarsa ke nan—kasar ta tarwatse, ta fada cikin yakin basasa—ka ga ba wanda zai tuhume shi da wani laifi tunda ba tsayayyiyar hukuma a Yemen.

Karin bayani