Minista na biyu ya kauracewa Gaddafi

Shukri Ghanem Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Mai na Libya, Shukri Ghanem

Majiyoyin tsaro a kasar Tunisia sun ce Ministan Mai na kasar Libya, Shukri Ghanem, ya sauya sheka bayan da ya isa kasar a ranar Litinin.

Gwamnatin Libyan dai ba ta tabbatar da labarin ba, ba ta kuma karyata shi ba.

Shi kuma Mista Ghanem bai bayar da wata sanarwa ba.

Idan har wannan labari ya tabbata dai, to kuwa shi ne zai kasance wani babban jami'in gwamnatin kasar na biyu da ya kauracewa gwamnatin Kanar Gaddafi, bayan da tsohon Ministan Harkokin Wajen kasar, Moussa Koussa, ya yi hakan a cikin watan Maris

Juma Al Gamaty shi ne mai magana da yawun kungiyar 'yan adawar Libyan da ke Burtaniya, ya kuma bayyanawa BBC cewa:

“Zan iya tabbbatar da cewa Mista Shukri ya sauya sheka.

“Majiyoyin dake kusa da iyalinsa sun ce matarsa da 'yarsa na zaune a wata kasa a nahiyar Turai, kuma sun tabbatar da cewa, baya tare da gwamnatin Gaddafi”.