Dokar hana shan taba zata soma aiki a China

Wani mutumin kasar China na busa taba a birnin Beijing Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane fiye da miliyan guda ne suke mutuwa a kowacce shekara a kasar China, sakamakon kamuwa da cutar dake da alaka da busa taba sigarin.

China wacce ita ce ta ukku a duniya dake da yawan masu shan taba sigari, ta dauki matakin haramta shan tabar a gidajen abinci da otel otel da tashoshin jiragen kasa da wuraren kallo da sauran wuraren da jama'a ke taruwa.

Ta dauki wannan matakin ne domin rage adadin mutanen dake mutuwa sakamakon kamuwa da cututtuka masu nasaba da shan tabar, wanda a halin yanzu ya kai fiye da mutane milliyan a kowacce shekara.

Wakilin BBC ya ce, dokar na karfafawa shugabannin kamfanoni, su gargadi ma'aikatansu game da hadarin dake tattare da shan taba sigari, amma ba tursasa masu kunna ta a ofisohinsu ba.