Dokar karancin albashi a kasar Hongkong

Majalisar dokokin kasar Hongkong Hakkin mallakar hoto CNS
Image caption Gwamnatin kasar Hongkong ta ce, so take ta rage gibin dake tsakanin mai kudi da talaka.

A yau ne wata doka mai cike da takaddama kan mafi karancin albashi, za ta soma aiki a kasar Hong Kong, daya daga cikin kasashen duniyar da ba su da wani takamaimai ka'ida kan tattalin arziki.

Gwamnatin kasar ta ce, so take ta rage gibin dake tsakanin mai kudi da talaka, wanda shine mafi girma a yankin Asia-Pacific.

Gwamnatin ta ce sabon tsarin mafi karancin albashin, na dala 3 da rabi a ko wacce sa'a, na nufin karin albashi ga ma'aikata da dama.

To amma daruruwan kungiyoyin kwadago sun gudanar da zanga zanga a jiya asabar, inda suke zargin kamfanoni da rage kudaden alawus da suka hada kudin hutu kafin kaddamar da sabuwar dokar.