Majalisar Dinkin Duniya na janye ma'aikata daga Tripoli

Ban Ki-moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ban Ki-moon, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya za ta janye ma'aikatan ta 'yan kasashen waje daga Tripoli, babban birnin kasar Libiya.

Hakan ya biyo bayan murtanin da jama'a suka mayar a fusace, bayan an sami rahotannin da ke cewa, daya daga cikin 'ya'yan jagoran Libiyar, Kanar Gaddafi, ya rasa ransa a wani harin da kungiyar tsaron NATO ta kai ta sama.

An kai hare hare a ofisoshin jakadanci masu yawa a Tripoli.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an wawashe ofisoshin ta a birnin.

Italiya ta yi Allah wadai da harin da aka kai a ofishin jakadancin ta a Libiyar, yayin da ita kuma Birtaniya ta kori jakadan Libiya daga kasar, a matsayin murtani ga hare haren da aka kaiwa ofishin jakadancin ta a Tripoli.

NATO ta musanta cewa ta na kai hari ne a kan wasu mutane a Libiyar.