Zargin kaiwa 'yan PDP hari a Zamfara

Jam'iyyar PDP
Image caption Jam'iyyar PDP

Wasu kusoshin jam'iyyar PDP mai mulki a jahar Zamfara, sun koka kan abinda suka kira: hare-haren bita da kullin da suka ce magoya bayan jam'iyyar ANPP - wadda a kwanan nan ta lashe zaben gwamnan jahar - ke kai wa gidajensu.

Wasu wadanda suka ce abin ya rutsa da su sun shaidawa BBC cewar, baya ga kone gidajensu, maharan - wadanda su ka ce matasan jam'iyyar ANPP ne - su kan kuma yiwa iyalansu duka, tare da raunata da dama daga cikinsu.

Jam'iyyar ANPP dai ta musanta zargin. Ta ce 'yan PDPn ne ke batar da kama su na kaiwa junansu hari, don dai kawai a shafawa ANPP

'Yan jam'iyyar ta PDP sun ce jami'an tsaro sun kasa daukar mataki akan lamarin.

Sai dai kwamishinan 'yan sandan jahar Zamfarar ya ce ba wanda ya kai masu rahoton cewa an kai masa hari.