Martanin kasashen duniyan kan kisan Osama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osama Bin Laden

Shugabannin siyasa da sauran al'ummomin duniya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da kashe jagoran kungiyar alka'ida Osama bin Laden. Dakarun Amurka na musamman dake Pakistan ne suka kashe Osama bin Laden, a wani makeken gidan da yake boye a garin Abbottabad dake arewacin birnin Islamabad.

Tsofaffin shugabannin Amurka George Bush, da Bill Clinton sun bayyana cewa wannan gagarumar nasara ce ga Amurka, da daukacin mutanen da ke neman zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya, da ma wadanda suka rasa rayukansu a harin ranar sha daya ga Satumba.

A nasa tsokacin, Fira Ministan Burtaniya David Cameroon, ya ce labarin mutuwar Osama bin Laden ka iya kawo saukin lamari ga al'ummar duniya, sai dai Mr Cameron ya yi gargadin cewa kisan ba shi ne zai kawo karshen barazanar da ake fuskanta ba daga masu tsattsauran ra'ayi.

Shi kuwa Prime Ministan Faransa Nicolas Sarkozy, jinjinawa Amurka yayi game da yadda suka jajirce wajen neman shugaban kungiyar al-Qaida inda ya bayyana kisan Osaman da cewa babban al'amari a duniya.

Anasa martanin, Fira Ministan Israela Benjamin Netanyahu, yace wannan gagarumar nasara ce da kuma 'yanci, da kuma tsari na kasashen da ke amfani da demokradiyya wajen yakar ta'addanci kafada da kafada.

Shi ma Fira Ministan New Zealand John Key, ya bayyana cewa:

"Osama bin Laden shi ne ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, ciki har da 'yan kasar New Zealand a sassan duniya, koda yake kawar dashi wajibi ne ya kawo karshen ayyukan ta'addanci ba, amma ina da tabbatar duniya ta koma tamkar sabuwa."

Sai dai anata martanin kungiyar Hamas ta yi kakkausar suka ne inda ta bayyana lamarin da cewa tamkar kisa ne ga jarumin shugaba.