Saudiyya ta yi marhabin da kisan Osama

'Yan tawayen kasar Libya sun yi marhabin da kisan Osama bin Laden, sun kuma yi kira ga Amurka da ta kawo musu dauki suma ta kashe Kanal Gaddafi.

Itama kasar Saudiyya, mahaifar bin Laden ta yi marhabin da kisan nasa, tana bayyana fatan cewa mutuwar tasa za tai matukar illa ga alqaeda da ayyukanta.

Can kuwa a yankin zirin Gaza, gwamnatin Hamas allawadai ta yi da kisan nasa inda ta kwatanta shi a matsayin balarabe mai da'awar yin jahadi.