A Pakistan aka kashe Osama Bin Laden

Osama bin Laden Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osama bin Laden

Dakarun Amurka na musamman dake Pakistan sun kashe Osama bin Laden, mutumin da ya kafa kungiyar al'qaeda. Shugaba Obama ne ya bada labarin kisan nasa a fadar White House.

Shugaba Obama ya ce an yi adalci kuma ba wani ba'Amurke ko farar hula da harin ya ritsa dashi.

Amurka tace kwararrun sojoji a bangaren yaki da ta'addacin ne suka je makeken gidan da yake a garin Abbot-tabad dake arewacin birnin Islamabad a cikin jiragen sama masu saukar angulu hudu.

An harbi Osama bin Laden a ka a musayar wutar da akai inda aka kashe karin wasu mutane uku cikin har da dansa.

Osama bin Laden ya mutu ne yana da kimanin shekaru 54 da haihuwa.