Kisan Osama: Abin kunya ga Pakistan

Wajen da aka kashe Osama bin Laden a garin Abbottabad na da nisan kilo mita daya ne kawai da makarantar sojoji dake birnin Islamabad, abinda ake ganin zai zama wani babban abin kunya ga gwamnatin Pakistan.

Mazauna garin sun yin mamakin jin cewa jagoran kungiiyar alqaedan na boye a kusa da su.

Kafin yanzu jama'a da dama sun yi tsammanin Osama bin Laden na boye a cikin wani kogo a yankin dake da tsaunuka a kusa da Afghanistan.

Yanzu haka dai anwa gidan da ake kashe Osaman kawanya.