Pakistan ba ta da masaniya kan harin da aka kaiwa bin Laden

Leon Panetta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban hukumar leken asirin Amurka, CIA, Leon Panetta

Hukumar leken asiri ta Amurka ta ce ba ta sanar da Pakistan shirin kai harin kama Osama bin Laden ba sabili da fargabar kada su fada ma shi.

Fadar White House kuma ta ce ba ya dauke da wani makami a lokacin da aka kai ma shi harin, amma dai ya ki ya mika kan shi ne.

Wakilin BBC ya ce gwamnatin Amurka ta dauki Pakistan a matsayin abokiyar ta mai matukar muhimanci a yakin da take da ta'addanci , amma tana zargin wasu a hukumar leken asirin kasar da goyon bayan masu tada kayar baya.

Tun da farko dai hukumar leken asiri ta Pakistan, ISI ta ce babban abin kunya ne ga jami'anta da suka gaza sanin cewa jagoran kungiyar ta al Qaeda, na zaune a wani gida mai kasa da nisan kilo mita daya da makarantar sojoji ta Pakistan.