Bikin Ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya

Wani dakin watsa shirye-shiryen Talabijin
Image caption Wani dakin watsa shirye-shiryen Talabijin

Jamhuriyar Niger ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin ranar 'yanci 'yan jarida.

Duk da cewa kasar Niger ta samu wani muhimmin ci gaba ta fannin daukar wasu dokokin da ke baiwa 'yan jaridar kasar yancin gudanar da aikin su, har yanzu akwai wasu matsaloli da suke fuskanta wadanda suka hada da karancin albashi da rashin ingantattun kayan aiki.

Wasu daga cikin matakan inganta aikin jaridar da gwamnatin Niger din ta dauka sun hada da ba kafofin yada labarai tallafin kudi, horo da kayan aiki daga baitalmanin kasa da kuma soke dokar da ke tisa keyar 'yan jarida zuwa gidan kaso.