Osama:Amurka ta bayar da mabambantan bayanai

Kakakin Amurka, Jay Carney Hakkin mallakar hoto White House
Image caption Amurka ta bayar da mabambantan bayanai kan Osama

Bayanai daga Amurka kan kisan da sojinta suka yiwa Osama Bin Ladan sun sabawa juna.

A yanzu Amurkan ta ce Osama Bin Laden baya dauke da wani makami a lokacin da aka kashe shi.

Kakakin gwamnatin Amurka Jay Carney, ya ce sojin Amurkan sun riski Osama ne a kan bene, inda suka harbe shi, amma baya dauke da wani makami a lokacin.

Wannan bayani dai ya ci karo da wanda fadar White House din ta bayar a baya, inda ta ce Osaman ya yi kokarin kare kansa da makami a yayin da sojin Amurkan suka kashe shi.

Jami'an gwamnatin Amurka dai sun yi amannar cewa Osama Bin Laden na zaune ne a cikin wani gida da ke Abbotabad kusa da Islamabad, cikin shekaru da dama da suka wuce.

A nata bangaren, Pakistan ta yi watsi da batun da ke fitowa daga Amurka cewa, rashin yarda da ita ne yasa Amurkan ta ki fada mata komai akan shirin kai farmakin kisan Osama bin Laden.