An kai karar gwamnatin Kaduna

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kai karar gwamnatin Kaduna

Wata kungiyar kare hakkin bil'adama a Najeriya ta kai karar gwamnatin Kaduna kotu a bisa abin da ta kira take hakkin bil'adama da take yiwa jama'a.

Shugaban kungiyar, Shehu Sani ya ce sun kai karar gwamnatin ne saboda yadda ta ki dage dokar hana fitar da ta sanya a jihar.

Ya ce mutane da dama sun kawo musu korafi kan yadda dokar ta hana su gudanar da ibada, da kasuwanci, abin da ke nuna take hakkinsu.

Sai dai gwamnatin jihar ta yi watsi da wannan batu, inda ta ce dokar ta magance matsaloli da dama a jihar.