An gargadi kasashen Afrika kan almubazzaranci

Image caption Kofi Annan

Yayinda shugabannin fiye da 900 su ka hadu a Cape Town domin taron tattalin arziki na duniya, ana gargadin cewar nahiyar Afrika na iya almubazzarantar da tattalin arzikin da ta samu a baya bayan nan.

Kofi Annan wanda ke jagorantar kwamitin ci gaban Afrika yayi tir da abinda ya kira ci gaban karancin shugabanci a nahiyar, sannan ya ce yalwar kashi biyar da rabin da ake sa ran Afrika za ta samu a wannan shekarar ba ta da wani tasiri babba a kan samar da ayyukan yi da kuma kawar da fatara.

Duk da cewa Kofi Annan, wanda shi ne shugaban Africa progress Panel - wacce ke kokarin ganin nahiyar ta bunkasa, ya ce kudurin bunkasa tattalin arzikin Afrika da kashi 5 da digo 5 abune mai kayatarwa, amma ya yi gargadin cewa shugabannin haniyar ba sa yin abin da ya kamata domin cimma wannan buri. Ya soki abin da ya kira karancin ci gaba - yawaitar dogaro kan kayayyakin masarufin da ba a sarrafa ba da kuma karancin zuba jari a fannonin sarrafa kayayyaki da ayyukan gina kasa.

Kuma a cewarsa, wannan ba ya taimakawa ko kadan wajen samar da ayyukan yi da fitar da miliyoyin jama'a daga kangin talauci.

Kofi Annan ya kuma kokawa kan abin da ya kira gibin shugabanci a nahiyar Afrika - ta yadda burin 'yan siyasa shi ne na darewa kan karagar mulki ido rufe, ba tare da maida hankali kan yadda za su bunkasa tattalin arziki ta hanyar habaka huldar kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar.

Ya yi tsokaci kan Kudancin Sudan, wacce nan da 'yan watanni kadan za ta zamo sabuwar kasa a nahiyar ta Afrika bayan kuri'ar raba gardamar da aka yi a farkon bana, inda ya yi gargadin cewa, kasar na bukatar shugabanni nagari domin amfana daga dimbin arzikin kasar noma da kuma ma'adanan da Allahn ya hore mata.