Matsalolin da su ka sa CPC ta sha kashi

Jam'iyyar CPC a Najeriya na daya daga cikin manyan jam'iyyun adawar da aka zaci za ta taka rawar gani a zabukan da suka gabata.

Wannan kuma ya dogara ne akan irin karbuwar da ake ganin sabuwar jam'iyyar ta samu, a kasa da shekara daya da kafuwarta.

Sai dai bayan kammala zabukan Najeriya da aka yi a watan jiya, jam'iyyar ta samu gwamna daya da kuma kujerun majlisun dakoki daga wasu jihohin kasar, wanda a da an zaci zata samu fiye da haka.

Sai dai wasu a cikin Jam'iyyar sun ce 'yan bani na iya ne suka kai Jam'iyyar suka baro.

Yayin da wasu ke ganin cewa rashin shawo kan matsalolin cikin gida ne suka janyo jam'iyyar ta kasa taka rawar a zo a gani.