ECOWAS na yaki da ta'addanci

Kasashen ECOWAS
Image caption Kasashen ECOWAS

A Najeriya wasu kwararru sun fara bitar wani kudirin yaki da ta`addanci, na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO.

Suna taron ne domin share wa kungiyar hanyar zartar da shi.

Kwararru daga nahiyar Afirka da kasashen Amurka da Turai ne ke wannan bitar.

Kudurin ya kunshi dabaru daban-daban, wadanda ake sa-ran mambobin kungiyar za su yi amfani da su wajen yaki da ta`addanci a shiyyar.

A yanzu haka dai yankin na yammacin Afirkan na fuskantar barazana iri-iri daga kungiyoyi irinsu Al Qaeda da Boko Haram da kuma MEND.