"Muna yunkuri samar da wuta".Arch Namadi

Yau ne mataimakin shugaban Nijeriya, Architect Muhammad Namadi Sambo ya kai ziyarar gani da ido a wata babbar tashar samar da hasken wutar Lantarki ta Olorun Sogo a Jihar Ogun.

Tashar dai tuni ta fara samar da hasken wutar lantarki.

Al'ummar kasar dai na korafin cewa har yanzu matsalar wuta ta addabi jama'a, duk da dubban miliyoyin dalolin da aka narkar a yunkurin samar da wutar.