Doka akan zaben shugabannin majalisar dattawan Najeriya

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya
Image caption Majalisar dokokin tarayyar Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da babban rinjaye da sauye- sauye a dokokin aikinta.

A karkashin sabuwar dokar da majalisar ta zartar a yau, sanatocin da suka fi dadewa a majalisar ne za a baiwa fifiko a kan sabbin sanatoci, idan an zo zaben shugabannin majalisar da kuma shugabannin kwamitocinta.

Masu sukar sauyin dai na ganin cewar, wani mataki ne na tabbatar da cewa shugaban majalisar Sanata David Mark, ya ci gaba da jan ragamar majalisar, kamar yadda Shugaba Goodluck Jonathan da Jam'iyyar PDP suke bukata.