Yunwa na barazana ga mutane kusan miliyan 3 a Nijar

Karancin abinci a Nijar
Image caption Karancin abinci a Nijar

A jamhuriyar Nijar mutane kusan miliyan 3 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci, saboda rashin kyaun daminar da ta wuce a wasu wurare.

Hukumar bincike a fannin karancin abinci ta kasar ce ta bayyana hakan.

A cewar kakakin hukumar, Malam Hamani Harouna, abubuwa dayawa ne suka janyo karancin abincin.

Sun hada da fari, da annobar kwari masu cinye amfanin gona, da kuma dubban 'yan gudun hijirar da suka koma kasar daga kasashen Libiya da Cote d'Ivoire, sakamakon tashe tashen hankula a can.

Gwamnatin kasar na bukatar sama da kudin CFA biliyan 70 domin tinkarar lamarin.

Nijar na fama da matsalar karancin abinci a kai a kai, musamman a 'yan shekarun nan, saboda karancin ruwan sama.