An daura yaki da rashawa a kotunan Nijar

A Jamhuriyar Nijar gwamnati ta fito da wani sabon shirin yaki da cin hanci da rashawa a cikin ma'aikatun shari'a.

Gwamnatin ta bude wani layin tarho, da kuma shafin Intanet, domin ba 'yan kasar damar tona asirin duk wani alkalin da ya karbi cin hanci, ko kuma duk wani wanda ya yi kokarin yin katsalandan da za ta iya yin tasiri a kan sauya shari'a.

A nata bangaren Kungiyar alkalan kasar ta Njar ta goyi bayan shirin,tana mai cewa zai taimaka wajen maido da martabar shari'a a kasar.

A yau shirin ke fara aiki, bayan kaddamar ad shi a jiya , wajen wani taron da ministocin ke yi a kowane mako.