'Yan siyasar Agadas sun fara neman kujerun Majalisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Jam'iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijar sun soma yakin neman zaben 'yan Majalisun Dokoki guda shida a Jihar Agadas.

Za a yi zaben ne a ranar 15 ga wannan watan da muke ciki domin cike gibin da aka samu a

Majalisun Dokokin kasar mai mambobi 113.

Kotun tsarin mulkin kasar ce ta soke zaben na Jihar Agadas a ranar 16 ga watan Maris da ya gabata.

Wannan ya biyo bayan wata kara da Jam'iyar adawa ta MNSD Nasara ta shigar gaban kotu, ta na kalubalantar wata 'yar takara ta Jam'iyar PNDS Tarayya da ta yi amfani da takardar kammala karatun diploma na jabu a cikin takardunta.