Farashin gangar mai ya fadi warwas

Hakkin mallakar hoto AP

Farashin danyan mai a duniya ya fadi da kashi goma cikin dari.

Ba'a taba ganin irin wannan faduwar ba cikin fiye da shekaru biyu.

Farashin gangar danyan mai a kasuwannin Amurka ya yi kasa da dala dari, lamarin da ya sa masu sharhi ke ganin hakan nada nasaba da bukatar man dake raguwa a kasar.

Wasu dalilan kuma sun hada da karfin dalar Amurka, da kuma yawan marasa aikin yi da suka karu a kasar, da kuma fargabar da ake da ita kan tafiyar hawaniya da ake samu a bangaren bunkasar tattalin arziki a fadin duniya