Fada ya barke a Kandahar na kasar Afghanistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hamid Karzai

Birni na biyu mafi girma a Afghanistan, wato kandahar dake kudancin kasar, ayyuka sun tsaya cik sakamakon mummunan fadan da ya biyo baya da ake zargin mayakan kungiyar Taliban da kaiwa akan gine gine gwamnati.

Hare hare akala guda shidda ne yan kurnar bakin wake suka kai.

Wuraren da aka kaiwa harin sun hada da hedkwatar gwamnan birnin, ofishin leken asiri da kuma ofishin rundunar yansanda

An dai ta jin fashewar abubuwa da kuma harben harben bindigogi a kusa da gidan gwamnan kandahar