Mutum hudu sun rasu a fadan Musulmai da Kirista a Masar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Jami'an kasar Masar sun ce akalla mutane hudu sun rasu, sannan da dama sun ji raunuka a wata arangamar da aka yi tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kirista a Kasar Masar.

Fadan wanda ya faru ne a kewayen garin Imbaba ya samo asali ne bayan da Musulmai suka kewaye wani chochi a yunkurin ceto wata mata da ake tsare da ita ba bisa doka ba, a saboda ta Musulunta.

Wadanda suka shaida afkuwar lamarin sun ce kimanin masu tsaurin ra'ayin addinin Islama dari biyar ne suka hallara a chochin Saint Mina, inda suka bukaci da a sako matar.

Musayar kalamai tsakanin mabiya addinan biyu, ya haifar da yin fito na fito a tsakanin su, inda suka fara musayar harbe harben bindigogi da jefa bama bamai da duwatsu.

Tuni dai aka aike da jami'an tsaro wurin, wadanda suka yi ta harbi a sama, suna kuma jefa barkonon tsohuwa.

A baya an yi ta samun rashin jituwa a tsakanin mabiya addinan biyu, duk da dai cewa sun hada kai a lokacin zanga zangar da ta hambarar da mulkin shugaba Hosni Mubarak.