Amurka ta tattauna da 'yan tawayen Libya

Image caption mayakan yan tawayen Libya

'Yan tawayen na Libya dai sun yi tattaki zuwa Amurka ne domin su yi kokarin ganin sun kara samun goyon baya ta fuskar siyasa da tattalin arziki.

Sun kuma je kasar ta Amurka ne domin su karbi kadarorin Libya wadanda aka sanyawa tankunkumi da yawansu ya kai biliyoyin daloli.

Fadar ta White House ta ce bangarorin biyu sun tattauna a kan yadda Amurka da kawancen kasashen duniya za su kara taimaka musu kuma sun sake yin kira ga Shugaba Gaddafi ya sauka daga kan mulki.

Kakakin gwamnatin Amurka, Mark Toner, ya ce gwamnatin ta Amurka za ta ci gaba da yin nazari a kan Majalisar Rikon Kwarya ta 'yan tawayen, wato Transitional National Council.

Sai dai ya ce wuka da nama na hannun jama'ar Libya wurin yanke shawara, ba kasashen duniya ba, a kan wanda zai jagoranci kasar nan gaba.

Amma Mista Toner ya ce Amurka ta dauki 'yan tawayen Majalisar Rikon Kwaryar a matsayin ingantattun, kuma halattattun, wakilan jama'ar Libya.

Sai dai Amurka da Birtaniya ba su bayyana 'yan tawayen a matsayin halattacciyar gwamnatin Libya ba kamar yadda Faransa, da Italiya, da Qatar suka yi.