Har yanzu akwai karancin mai a arewacin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa har yanzu ana ci gaba da fuskantar matsalar karancin man fetur da kuma karuwar farashin sa a wasu Jihohin Arewacin kasar.

Masu ababen hawa kan dauki lokaci mai tsawo a layuka a gidajen mai domin shan man. Manyan masu ruwa da tsaki a harkar man dai na dora laifin matsalar ne a kan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a karshen watan da ya gabata, amma wasu talakawa na cewa da gangan aka haddasa matsalar domin wasu su amfana. Karanci da kuma tsadar man fetur a Najeriya dai kan haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi sabo da karuwar wahalar sufuri.