Majalisun Pakistan sun ce a sauya matakan tsaro

Image caption Majalisar dokokin Pakistan

Wani zaman hadin gwiwa da majalissun dokokin Pakistan suka yi, yayi kira da gagarumin rinjaye akan a dau matakan sauya tsarin tsaro, da kuma manufofin huldar kasar da kasashen waje.

Zaman majalisar ya kuma nemi a kawo karshen kai hare-hare da jiragen sama masu sarrafa kansu da Amurka ke yi a kasar, kana kuma a kawo karshen amfani da kasar ta Pakistan da dakarun NATO ke yi wajen safarar da kayan aiki zuwa Afghanistan.

Majalisar ta kuma nemi a yi bincike na musamman akan harin dakarun Amurka, da ya kai ga kisan Osama bin Laden, lamarin da majalisar tace, ya keta haddin kasar ta Pakistan.