CPC ta nemi a soke zaben shugaban kasa

A Najeriya, Jam'iyar adawa ta CPC ta shigar da kara yau a gaban kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa, inda take kalubalantar zaben shugaba Goodluck Jonathan, a matsayin wanda hukumar zaben INEC ta ce shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a watan jiya.

Jam'iyyar ta CPC ta ce hujjojinta na shigar da karar sun hada da zargin tafka magudi, da kuma rashin bin dokokin zabe, inda ta ce zata gabatar da shaidu 151 a karar da ta shigar.

Da ma dai dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta CPC , Janar Muhammadu Buhari, ya ce shi a matsayinsa, ba zai shigar da kara kan sakamakon zaben ba, sai dai jam'iyyarsa, in ta ga dama.