Obama ya ce a binciki buyar Bin Laden

Osama Bin Laden Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osama Bin Laden

Shugaba Obama yayi kira ga gwamnatin Pakistan da ta gudanar da bincike, domin gano wadanda suka taimakawa Osama bin Laden a gidan da ya boye, kafin sojan kundumbalar Amirkan su hallaka shi a makon jiya.

Ya bayyana hakan ne a cikin hira da wani gidan talabijin.

To amma kuma in ji shugaba Obaman, ba shi da wata shaidar da ke nuna cewa, wasu jami'an gwamnatin Pakistan sun tallafawa bin Laden.

Pakistan dai ta yi watsi da zargin cewa, ita ce ta ba Osama bin Laden mafaka.

Haka nan kuma tuni ta bada umurnin a gudanar da bincike a kan gazawar hukumomin leken asirinta, wajen gano shugaban na al Qaeda.