ECOWAS za ta yi nazari kan yaki da ta'addanci

A yau ne kwararru daga kasashen yammacin Afrika za su fara wani taro na kwanaki biyu a Abuja domin nazari akan wani daftarin Kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO, kan yaki da ta'addaci.

A 'yan shekaru nan wasu kasashen dake Kungiyar sun yi ta fuskantar aikace- aikace dake da nasaba da ayyukan ta'addanci wadanda suka hada da tashin bama bamai, da dai sauransu.

Wannan lamari ya sa Shugabannin ta fuskar tsaro shakkar bullar barazana game da wadannan aiyuka da suka yi kama da ta'addanci.

Kwararrun sun bayyana cewa daga cikin abubuwan dake kawo ta'addanci shine rashin adalci, wanda za'a iya kwatantawa ta fuskoki da dama.

Sun kuma ce, curewa wuri guda da duniya ta yi ya sa matasa sun fara lakantar yadda ake kera makaman da ake amfani dasu domin aikata ta'addanci.