Mutane 12 suka mutu a rikicin Masar

Rikici tsakanin Musulmi da Kirista a Masar Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Rikici tsakanin Musulmi da Kirista a Masar

Hukumomi a Masar sun ce sun kama mutane dari da casa'in , bayan wani mummunan tashin hankali tsakanin Musulmi da Kirista jiya da dare, kuma wadanda aka kaman, za a gurfanar da su a gaban kotun soja.

Gidan talabjin na Masar ya ce, a yanzu yawan mutanen da suka mutu ya kai goma sha biyu, wasu kuma sama da dari biyu sun jikkata a lokacin rikicin.

Rikicin ya barke ne lokacin da wasu Musulmi suka kewaye wani cocin Kibdawa - ko kuma Coptic - a kokarinsu na kubutar da wata mata da suke zargin ana rike da ita ba da son ranta ba, bayan ta Musulunta.

Praministan Masar din, Essam Sharaf ,ya soke wata ziyara zuwa yankin Gulf, domin jagorantar wani taron majalisar ministoci na gaggagwa .