Pakistan ta ce bata da masaniyar Osama na kasar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Idan an jima ne ake sa ran cewa Fira Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani zai yi wa Majalisar Dokokin Kasar jawabi kan mamayar da Amurka ta kai wadda ta yi ajalin Osama Bn Laden a makon da ya gabata.

Wannan jawabin zai zo ne bayan jerin tambayoyin da suka taso game da yadda Osama Bn Laden din ya yi rayuwar shekara da shekaru a garin Abbotabad ba tare da Jami'an Pakistan sun sani ba.

Duk da dai cewa tun a baya ana zaman ta ciki na ciki ne a tsakanin Amurka da Pakistan, yanzu kuma rasuwar Shugaban Kungiyar Al Qaeda, Osama Bn Laden ta kara tsaurara lamarin.

Duk da dai Amurka ta na takatsantsan wajen zargin Pakistan da hannu kan kasancewar Osama a birnin Abbotabad na wasu shekaru kafin rasuwarsa, inda ta ke shakkar ko yana samun goyon bayan wasu a gwamnati, Pakistan din za ta so nuna cewa sam bata da wata masaniya game da wannan al'amari.

Pakistan dai ta ce idan har wani mamba na gwamnati ko soji ko kuma Hukumar leken asirin ta na da masaniyar cewa Osama Bn Laden na kasar, da tuni ta dauki mataki.

A ranar lahadi ne dai Shugaba Obama yayi kira ga gwamnatin Pakistan da ta gudanar da bincike dangane da irin goyan bayan da Osama bn Laden ya samu a lokacin da yake boye.