An koka da yanayin gidan kaso a Nijar

A jamhuriyar Nijar dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam din nan, Malam Nuhu Arzika, ya koka a kan halin da fursunonin gidan yari na birnin Yamai ke ciki.

A cewar Malam Nuhu Arzikan wasu fursunonin kan kwashe shekaru da dama, ba tare da an yi musu shari'a ba, sannan yanayin rayuwarsu ya tabarbare ; abin da yake ganin ya saba ma doka.

Malam Nuhu Arzika ya bayyana hakan ne yau din nan a Yamai yayin wani taron manema labarai da ya kira, bayan sako shi daga gidan kason na Yamai, inda ya kwashe kusan watanni uku. Amma ministan shari'a na kasar ta Nijar Malam Marou Amadou ya ce gwamnati za ta duba lamarin a cikin gaggawa.