Binciken kudaden haram a Cote d'Ivoire

Tsohon shugaba Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsohon shugaba Laurent Gbagbo

Masu shigar da kara a Switzerland sun fara gudanar da bincike kan zarge zargen da suka shafi halatta kudaden hara, kamar yadda sabuwar gwamnatin Cote d'Ivoire ta bukata.

Jami'ai basu ambato sunan kowa ba.

Sai dai lauyan dake wakiltar shugaban Cote d'Ivoire din, Alassane Ouattara a Geneva, ya ce an shigar da kara ne a kan tsohon shugaban kasar, Laurent Gbagbo, da uwargidansa, da kuma na kurkusa da shi. A makon da ya gabata ne mahukuntan kasar Switzerland suka hana taba kadarorin da aka danganta da Mr. Gbagbo, wadanda darajarsu ta kai dala miliyan tamanin.