'Daruruwa' sun hallaka a hadarin jirgin ruwan Libiya

'Yan gudun hijirar Libiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijirar Libiya

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, ta samu rahotannin dake cewa, wani jirgin ruwa dauke da baki 'yan ci-rani ya nutse a gabar ruwan Libya, a makon daya gabata, kuma mafi yawansu sun rasa rayukansu.

Shaidu sun fadawa hukumar cewa, jirgin ya yi dai-dai, kuma sun ga gawarwaki da yawa a cikin ruwan.

A wani lamarin na dabam kuma, kungiyar tsaron NATO ta musanta rahotannin da ke cewa, ta kasa kai dauki ga wani jirgin ruwan da ya sami kansa cikin mawuyacin hali.

Jirgin yana dauke ne da 'yan ci-rani daga Afirka, wadanda ke tserewa fadan da ake a Libya.

An ce daga bisani sama da sittin daga cikinsu suka hallaka.