Gwamnan jihar Imo ya rungumi kaddara

Cif Ikedi Ohakim
Image caption Cif Ikedi Ohakim na daga cikin gwamnoni kalilan da suka fadi zabe

A Najeriya gwamnan jihar Imo da ke kan mulki, kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan da ya gabata, Cif Ikedi Ohakim ya rungumi kaddara, dangane da faduwa zaben da ya yi.

Har ma ya taya wanda ya ci zaben murna, kuma ya bayar da tabbacin ba zai je kotu kan batun zaben ba. Cif Rochas Okorocha na jam'iyyar APGA ne ya kayar da Ohakim - wanda shi ne gwamna mai ci bayan anyi sa'insa mai tsanani a gaban akwatinan zabe.

Kwamishinan yada labarai na jihar Imo, Nze Elvis Agukwe, wanda ya fayyace matsayin gwamnan jihar a kan zaben, ya shaida wa BBC cewa:

"Cif Dokta Ikedi Ohakim, ya aike da sakon taya murna ga Cif Rochas Okorocha, wanda ya sami nasarar zaben. Ya kuma bayyana fatan alheri ga jama'ar jihar Imo".

'hanya ce ta yi wa jama'armu aiki'

Kwamishinan ya kuma ce gwamna Ikedi Ohakim ya yanke shawarar hakan ne kuwa, don ya nuna halin dattaku da kishin kasa. "Saboda gwamnan ya yi amanna cewa, bai kamata sha'anin siyasa ya kasance wani abu da za a gudanar ta hanyar a mutu ko ai rai ba. Ya yi amanna siyasa wata hanya ce ta yi wa jama'armu aiki. Kuma tun da jama'ar jihar sun yi zabinsu, ya amince da haka". "Gwamnan na jihar Imo mai barin gado dai, ya yanke shawarar ba zai je kotu ya kalubalanci sakamakon zaben ba", a cewar Nze Elvis Agukwe.

Ta kowane hali dai, masu lura da al'amura na ganin inda duk aka gudanar da zabe na gaskiya da adalci, kuma aka bar talakawa suka yi zabinsu, irin wannan mataki na rungumar kaddara ba zai zama wani abin al'ajabi ba.