Amurka ta taimaka wajen kafa al-Qaeda - Pakistan

Yusuf Raza Gillani Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fira Minista Yusuf Raza Gillani ya kare jami'an leken asirin Pakistan

Fira Ministan Pakistan Yusuf Raza Gilani, ya ce Amurka ta taimaka wajen kafuwar kungiyar al-Qaeda lokacin da Tarayyar Soviet ta mamaye kasar Afghanistan.

Mista Gilani yana magane a gaban Majalisar Dokokin Pakistan game da harin da sojojin kundumbalar Amurka suka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Osama Bin Laden a makon da ya gabata.

Ya bayyana kalaman kariya ga tarihin Pakistan a fagen yaki da ta'addanci, yana mai bayyana "irin asarar" da hakan ya haifarma da kasar ta fuskar soji da kuma fararen hula.

Ya kuma karyata da babbar murya zargin da ake yi na cewa akwai masaniyar Pakistan wajen zaman Bin Laden a kasar.

"Zargin hadin baki ko rashin kwarewa bai kamata ba," kamar yadda ya shaidawa 'yan Majalisar.

Ya ce harin da Amurka ta kai ya keta 'yancin Pakistan na kasa mai zaman kanta, sannan ya ce Amurka ta taimaka wajen kafuwar al-Qaeda lokacin da Tarayyar Soviet ta mamaye Afghanistan.

Image caption Jama'a da dama a Pakistan sun yi Allah wadai da Amurka

Kuma harin da aka kaiwa Afghanistan a shekara ta 2001, ya taimaka wajen watsuwar mayakan kungiyar ta al-Qaeda zuwa makwaftan kasashe.

"Ba mu gayyaci al-Qaeda zuwa Pakistan ba, kamar yadda ya nanata," ya kara da cewa gaza sanin inda Bn Laden yake shekara-da-shekaru gazawa ce ta "ayyukan leken asiri.... na Hukumomin leken asiri na kasashen duniya ba ki daya".

Jawabin na sa dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna shakku kan yadda jagoran na al-Qaeda ya zauna a wani gida a garin Abbottabad kusa da birnin Islamabad ba tare da an gano shi ba.

A ranar Lahadi, shugaban Amurka Barack Obama, ya nemi Pakistan da ta binciki wadanda yace na da hannu wajen boye Osama a kasar. Mista Obama ya ce akwai bukatar gano ko akwai hannun jami'an gwamnatin kasar a ciki.

Ana nuna matukar damuwa kan cewa wani daga cikin jami'an Hukumar leken asiri ta Pakistan (ISI), wacce ke de alaka da kungiyoyin masu tayar da kayar baya, sun san inda Bin Laden yake boye.

Sai dai Mista Gilani ya gayawa 'yan Majalisar Dokoki cewa Hukumar ta ISI na da cikakken goyon bayan gwamnati.

Ya kuma kara da cewa Amurka na nan a matsayin babbar kawar Pakistan.