Pakistan ta kare kanta a batun Bin Laden

Praministan Pakistan Yusuf Raza Gilani, ya yi jawabi ga majalisar dokokin kasar a kan harin da sojojin Amurka suka kai a makon jiya, inda suka hallaka, Osama Bin Laden.

Praministan ya yi watsi da sukar da ake yi wa Pakistan din, cewa akwai wasu manya jami'an gwamnati da suka taimaka wajen boye Bin Laden.

Mr Gilani ya ce ba wata kasa a duniyar nan da kuma hukumomin tsaro da suka yi namijin kokari wajen yaki da kungiyar Al-Ka'ida, irin hukumar leken asirin kasarsa ta, ISI da kuma dakarun tsaron kasar.

Mr Gilani ya ce ba zai bari wasu kasashe su dora wa Pakistan alhakin gazawar kwarewar aikin leken asirinsu ba.