Tallafin kudi don biyan diyya a Japan

Tashar Fukushima Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a biya Japanawa diyya

Kamfanin da ke aiki a tashar nukiliya ta Fukushima da ta lalace sakamakon girgizar kasa da tsunami a Japan, wato Tepco, ya bukaci tallafin kudi daga gwamnatin kasar.

Kamfanin ya ce zai yi amfani da kudin ne domin biyan diyya ga mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon bala'in da ya aukawa tashar.

Shugaban kamfanin na Tepco Masataka Shimizu ya ce halin rashin kudin da kamfanin ya tsinci kansa a ciki ya yi matukar muni.

Ya yi gargadin cewa, muddin hakan ya ci gaba, to zai shafi biyan diyya ga mutanen da lamarin ya rutsa da su.