An kafa kwamati kan rikicin zabe a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption An kafa kwamati kan rikcin siyasar Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti da zai binciki tashe-tashen hankulan da suka faru a wasu jihohin arewacin kasar, biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Afrilu.

Kwamitin, mai mambobi 22 zai kasance karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Lemu, kuma tsohon jojin kotun koli, mai shari'a Samson Uwaifo ne mataimakinsa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin babban sakataren gwamnatin Najeriya, ta ce kwamatin zai kuma gudanar da bincike kan rikicin siyasar da ya faru a jihar Akwa Ibom gabanin babban zaben kasar.

Sanarwar ta ce shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan ne zai kaddamar da kwamatin a gobe Laraba.